Sanata Bukola Saraki ya mayar da martani kan kwace gidajensa

Sanata Bukola Saraki ya mayar da martani kan kwace gidajensa

Tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP Bukola Saraki, ya ce ya yi imani ba a gabatar wa alkalin babbar kotun tarayya ta Ikoyi cikakken matsayin doka ko bayanan gaskiya game da batun kwace kadarorinsa ba.

A cewarsa tabbas ba a sanar da kotun komai game da wani umarni na wata babbar kotun tarayya a Abuja da ke hana EFCC daukar wani mataki na kwace wannan kadara da ake magana a kanta ba, har sai ta yanke hukunci kan wata kara da ke gabanta.

Hukumar EFCC ta ce lauyanta Nnaemeka Omewa ne ya gabatar da bukatar a gaban mai shari’ah Mohammed Liman wanda ya amince tare da bayar da umarnin kwace kadarorin guda biyu a matakin wucin gadi.

Shugaban sashen hulda da kafofin labarai na hukumar, Wilson Uwujarem ya tabbatar wa BBC da sahihancin labarin.

A lokuta da dama dai, wasu na sukar yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da cewa a kan ‘yan adawar kasar yake karewa, zargin da mahukuntan Abuja suka sha musantawa.

Ko a lokacin da yake shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki ya fuskanci shari’ah kan zargin sharara karya wajen bayyana dukiyar da ya mallaka, kafin kotu ta wanke shi daga laifi.

Ita dai Hukumar EFCC ta ce ta shaida wa kotun zargin cewa tsohon shugaban majalisar dattijan ya mallaki kadarorin biyu ne ba ta hanyar halas ba lokacin da yake gwamna a jihar Kwara.

EFCC ta ce ya fitar da naira na gugar naira har biliyan 12 daga asusun jihar ya kuma shigar da su cikin asusun ajiyar daya daga cikin mataimakansa na musamman, Abdul Adama a lokuta daban-daban.

Sai dai a martanin da ya mayar ta shafinsa na Twitter, Bukola Saraki ya ce ya yi imani ba a sanar da kotun cewa kadarorin da ake magana kansu, kotu ta yanke hukunci kansu ranar 6 ga watan Yulin bara ba.

Ya kara da cewa Kotun Koli ta ayyana cewa hanyar da aka samu kudin sayen ba na haramiya ba ne kamar yadda masu gabatar da kara suka yi ikirari.

EFCC ta ce kadarorin sun kunshi gini mai lamba 17A a kan titin McDonald da ke yankin Ikoyin jihar Legas wanda kuma take zargin an saye su ne da dukiyar da aka samu ta hanyar da ba ta halaliya ba.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: