Saudiya: An kai hari kan tankunan dakon mai

Saudiya: An kai hari kan tankunan dakon mai

Mahukuntan Saudiya sun ce matakin kai wa tankunan dakon man fetur din kasar hari, yunkuri ne na tayar da zaune tsaye a tsakanin kasashen yankin Gulf.

Ana yunkurin  takalar fada da kuma ka iya tayar da wutar rikici acewar wani mai magana da yawun rundunar kawance da Saudiya ke jagoranta a Yemen . An dai wayi gari a jiya Alhamis da labarin harin da tuni ya janyo martani daga kasashen duniya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a gudanar da wani zama na gaggawa kan batun. Babban magatakarda na Majalisar Antonio Guterres, ya baiyana takaici inda ya ce ba za a lamunci irin wannan yanayi na son tayar da zaune tsaye ba a yankin na Gulf.

 A watan Mayun wannan shekarar ma, an kai hari kan tankunan dakon man fetur hudu na Saudiyan a kusa da hadaddiyar Daular Larabawa inda aka zargi Iran da hannu, sai dai gwamnatin Tehran ta musanta zargin inda har ta nemi a gudanar da bincike. DW

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: