Super Falcons zata samu dolar Amurka miliyan biyu

Super Falcons zata samu dolar Amurka miliyan biyu

A gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta mata da za’ayi a wannan shekarar, hukumar wasan kwallon kafa ta duniya ta bayyana irin kudin da ko wace kasa zata samu.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Super Falcons, Thomas Dennerby, ya bayyana cewa zasuyi kokari buga wasan kusa dana karshe na gasar. inda ya kara da cewa inhar komai ya tafi yadda ya kamata kungiyar ta Super Falcons zata dawo gidan da dollar Amurka miliyan 1,600 sakamakon buga wasan kusa dana karshe a yayin da zasu kara samu $400,000 inhar suka shiga cikin jerin kungiyoyi uku mafiya kokari a gasar.

Bayyanan sun fito daga shedikwatar shukumar wasan kwallon kafar ta duniya wadda ofishin ta yake kasar Switzerland,  sun ce wadda tazo ta daya a gasar zata samu $4 miliyan a ya yin da wadda tazo ta biyu zata samu $ 2.6 milliyan.

Duk wadda suka buga wasan kusa dana karshe zasu samu $ 1.6 miliyan zuwa dollar $ miliyan biyu, a inda duk kugiyar data buga wasan daf dana kusa dana karshe zata samu dolar Amurka 1.45 inda kuma zagaye na 16 zasu samu dolar Amurka miliyan daya.

Kungiyoyi takwas da za’a fara fitarwa ko waccan su zata samu dalar Amura $750,000.

Kungiyar kwallon kafa ta Super Falcons wadda take samun tikitin buga gasar ko wane lokaci tana rukuni na A tare da mai masaukin baki kasar France da Korea Republic da kuma Norway.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: