Yadda Boko Haram ta kashe masu janaza 23 a Borno

Yadda Boko Haram ta kashe masu janaza 23 a Borno

Bayanai sun nuna cewa da misalin karfe 10 na safe ne dai ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne a kan babura suka yi dirar mikiya a kan wasu mutane da ke kan hanyarsu ta dawowa daga makabarta bayan yin sutura, yankin Nganzai da ke gefen birnin Maiduguri.

‘Yan kungiyar sun bude wa mutanen da ke dawowa daga garin Badu Kuluwa da ke kusa da Goni Abachari wuta irin ta kan mai uwa da wabi, inda su ka kashe mutum 23

‘Yan sintiri ne suka dauko gawarwakin mamatan bayan da wadanda suka samu suka tsira sun sanar da su.

Maharan Boko Haram dai na yawan kai hare-hare yankin na Nganzai, inda ko a watan Satumbar da ya gabata sai da ‘yan kungiyar suka yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas a yankin.

Har wa yau, ‘yna Boko Haram din sun yi awon gaba da shanu da sauran nau’in dabbo daga kauyuka guda biyu da ke yankin na Nganzai a watan Satumba.

Rahotanni na cewa da yammacin ranar Alhamis din da ta gabata ma sai da ‘yan Boko Haram din suka kai farmaki wani sansanin ‘yan gudun hijra da kone wani sansanin sojoji da ke wajen birnin na Maiduguri duk a kokarin satar abinci.

A ranar Talatar nan ne dai rikicin na Boko Haram ke cika shekara 10 cif-cif da fara shi, tun bayan kashe shugaban kungiyar Jama’atu Ahlussunnah Lidda’awati Wal Jihad da aka si sani da Boko Haram, Muhammad Yusuf, a ranar 30 ga watan Yulin 2009.

Rikicin Boko Haram ya fadada zuwa kasashe masu makwabtaka da Najeriya kamar Chadi da Niger da Cameroon, inda kididdiga ta ce an yi asarar rayuka kusan 30,000 sannan fiye da mutum miliyan biyu sun bar matsugunansu.

BBC

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: